Tasawwuf

Tasawwufi ya ginu ne da kalmomin da suke magana da Allah, ba da mutane ba.

wanda ya fahimci harshen ma’ana, sai ya ji cewa duk kalmar sufi tana da haske daga cikin zuciya.

Tasawwufi ba magana ce ta zahiri ba, magana ce ta ma’ana da ishara.

Haka Wanda bai san harshen ma’ana ba, zai zargi mai tasawwufi da sabo; alhali yana magana ne da zuciya, ba da harshe ba.

A cikin Tasawwufi, kalma tana da fuskoki

Haka zalika Sufaye suna amfani da harshen ma’ana, domin magana ta ruhi ba ta tafiya kai tsaye kamar ta hankali.

Harshen ma’ana yana cike da sirri.

Imam al-Ghazali ya ce:

“Mai wuyar magana shi ne wanda ya taɓa sirrin Allah, domin kalmarsa tana fita da zafin ma’ana.”

 tasawwufi yana buƙatar fahimta kafin hukunci, domin ba kowanne kalma ake auna ta da ƙa’idar zahiri ba.

Allah yana cewa:
سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الآفَاقِ وَفِي أَنْفُسِهِمْ

“Zamu nuna musu ayoyinMu a cikin sararin samaniya da cikin kansu.”

Sufi yana karanta wannan ayar cikin zuciyarsa, ba kawai cikin littafi ba.

Saboda haka, harshen sa harshen ruhi ne, ba harshen hayaniya ba.

اللهم ارزقنا فهما عن أوليائك، وارزقنا أدبا مع كلام أهل معرفتك. 

“Wanda ya fahimci harshen ma’ana, ya gane cewa ba duk abin da ya ji ake rarraba shi da harshe ba; wasu abubuwa ana jin su ne da ruhi.”

🕊️ 🕊️ 🕊️ 🕊️

Comments

Popular posts from this blog

Terrorism Has Nothing To Do With Religion

نفحات الفيض في رحلة كانواْ

MUSHRIY