Zuwan Sheikh al-Hādi zuwa Ghana da Yadawar Faidah
Bayan Sheikh al-Hādi bn Sidi Mulūd Fāl ya yada ilimi da ruhi a yankin Najeriya, labarinsa ya wuce iyakokin Arewa, ya ketara zuwa Ghana. Wannan tafiya ba ta kasance kawai hijirar malami ba, a’a, ta kasance tafiyar haske wato hasken ma’rifa. A lokacin, Ghana tana da cibiyoyi masu ruhi na Tijāniyya amma ba ta kai ga zurfin fayḍah (فَيْضَة ambaliyar ruhaniya) kamar yadda aka samu daga gidan Kaolack ba. Saboda haka Allah Ya zabi Shehu al-Hādi a matsayin hanyar watsa wannan haske. Lokacin da ya isa kasar Ghana, jama’a suka karɓe shi da girmamawa. Ya kafa majalisu na zikiri da karatun jawāhir al-ma‘ānī, yana jawo hankalin mutane zuwa ga sirr al-faidah wato sirrin da ruhin Sheikh Ibrāhīm Niasse yake rabawa ta cikin salasilarsa. A cikin ɗaya daga cikin bayt (بيت) nasa, Sheikh al-Hādi ya ce: سَقَانِي حَبِيبِي كَأْسَ الوِصَالِ، فَغِبْتُ عَنِ العَالَمِينَ بِالْكَمَالِ “Ma’abocin so na ya bani kofi na haɗuwa (da shi), sai na gushe daga duniya saboda cikakkiyar haɗuwa.” A nan “كأس ا...